Shugaba Isoufu ya ce abinda ya sa ya je Diffa shi ne domin ya gaida askarawan kasar, da kuma basu kwarin gwiwar kare kasar da kuma kare al'umma da kuma dukiyoyinsu
Al'ummar Diffan dai sun yabawa Shugaban Kasar, kuma sun bayyana gamsuwarsu da abinda yake musu
Shugaban ya ziyarci rundunar soji ta 52 a garin na Diffa , daga bisani kuma ya ziyarci mutanen da hare- haren Boko Haram ya shafa a babban asibitin garin.
Boko Haram ta kai hare hare garin Diffa a kwanakin da suka gabata.ABNA